Alhassan Doguwa ya bayyana dalilin da yasa bai halarci taron masu ruwa da tsaki na APC ba a Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa sardaunan Rano (OON) yace ba zai sake cewa komai ba kan rikicin dake tsakanin sa da Murtala Sule Garo sakamakon kiraye – kiraye da Shugabannin jam’iyyar APC na kasa su kayi masa.

 Shugabannin jam’iyyar APC taki kasa yanzu haka sun umarci Alhassan Ado Doguwa da kada ya sake cewa komai akan rikicin saboda kokarin da suke na shawo kan rikicin.
Alhassan Ado Doguwa ya bayyana hakan ne cikin wata Sanarwa da hadinmin Shugaban Majalisar wakilai Auwal Ali Sufi ya sanyawa hannu Kuma ya aikowa kadaura24.
Talla
Dangane da musayar kalamai da ake yi a tsakanin ya’yan jam’iyyar APC da masoya da Magoya an bukaci ya dakatar da dukkanin wasu maganganu, akan batun Kuma har yanzu shi dan jam’iyyar APC ne” . A cewa sanarwar
Ya kuma ce yanzu haka yana tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, shi ne dalilin da yasa bai halasci taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC ba daka gudanar a Gidan gwamnatin jihar kano yau lahadi.
 Yanzu haka yana tare da dan takarar shugaban kasa Sen Ahmad Bola Tinubu Wanda ya Kira shi birnin tarayya Abuja domin warware rikicin cikin ruwan sanyi”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari

  Rahotanni daga Katsina na cewa gwamnan jihar Katsina Dikko...

Zargin almundahana: ICPC ku fita daga harkokin Siyasar Kano – Kungiyar Ma’aikatan KANSIEC

Daga Hafsat Abdullahi Darmanawa   Kungiyar ma'akatan wucin gadi da suka...

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...