Zargin ajiye kudi a gida: Gwamnatin kano tace zata ɗauki matakin Shari’a akan jaridar Sahara Reporters

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Gwamnatin Jihar Kano tayi martani game da wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Sahara Reporters ta wallafa, wadda ta bayyana cewa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana daga cikin gwamnoni uku da aka samu Maƙudan Ƙuɗaɗe a gidajensu.

 

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano kwamarade Muhammad Garba shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.

 

Muhammad Garba yace labarin bashi da tushe ballantana makama dan haka al’umma suyi watsi dashi.

 

Ya ƙara da cewa bayan sanarwa da hukumar EFCC ta fitar a kan wasu Gwamnoni 3 da tace tana sanya idanu akansu, bata bayyana sunan Gwamnonin ba.

Talla

To amma jaridar Sahara Reporters ta kama sunan Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda kuma hakan ya saba da ka’ida.

 

Muhammad Garba yace wajibine Jaridar ta Nemi yafiyar Ganduje bisa abinda ta wallafa wanda ba gaskiya bane, inda yace Idan basu nemi afuwar gwamnan ba to zasu dauki matakin Shari’a akan jaridar.

 

Muhd Garba yace gwamnatin jihar kano tana daga cikin jihohi kalilan da suke iya bisan albashi, Inda ya ko a lokacin da Sahara Reporters ta rubuta labarin tuni gwamnatin ta fara biyan ma’aikata albashinsu na watan October

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari

  Rahotanni daga Katsina na cewa gwamnan jihar Katsina Dikko...

Zargin almundahana: ICPC ku fita daga harkokin Siyasar Kano – Kungiyar Ma’aikatan KANSIEC

Daga Hafsat Abdullahi Darmanawa   Kungiyar ma'akatan wucin gadi da suka...

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...