Daga Rukayya Abdullahi Maida
Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso a shirye yake ya karbi Hon. Alasan Ado Doguwa ya koma tafiyar kwankwasiyya kamar yadda ya yi ta a baya.
Hakan ya fito ne daga bakin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Rano, Bunkure da Kibiya a wata hira da manema labarai a Kano.
Yace lokacin da Kwankwaso ya sami labarin koken da Doguwa ya yi cikin wani shiri na kai tsaye da kadaura24 ta kawo shi lokacin da yake ganawa da Magoya bayan sa, yace yanzu haka Kwankwaso ya kafa wani kwamiti mai karfi domin zuwa a yiwa Alhassan Ado Doguwa ta’aziyyar rashin mahaifin sa.

” Kwamitin da Sanata Kwankwaso ya kafa ya hadar jagoran kwamitin Sen. Rufa’i Sani Hanga, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da shugaban jam’iyyar mu ta jiha, Hon. Umar Haruna Doguwa da Hon. Sarki Aliyu Daneji a matsayin ‘yan tawagar.” Inji Rurum
Ya ce siyasa harkace ta wa yafi yawan mutane, don haka a shirye muke domin shiryawa da yin sulhu da tsohon abokanmu na Siyasa kuma na zumunci a yunkurinmu na ganin mun cimma manufar samar da sabuwar Najeriya.
Hon. Kabiru Alhassan Rurum wanda ya tabbatar da cewa yana wannan magana ne da sani kuma da yawun jagoran su Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya bada tabbacin zasu yi aiki tukuru domin samun nasarar shiryawa da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa Alhassan Ado Doguwa.
Rt. Hon. Rurum ya tabbatar da cewa za su kai ziyarar ta’aziyyar ne a madadin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP H.E Rabiu Musa Kwankwaso da wuri domin cika sharuddan da Hon. Alhassan Ado Doguwa da kuma tabbatar da cewa manyan kifi na cikin gidan yanar gizon mu nan bada jimawa ba.