Daga Kamal Yahaya Zakaria
Hajiya Rabi Abdullahi, mahaifiyar mataimakin ɗan takarar gwamna na NNPP a jihar Kano, Comrade Aminu Abdulsalam ta rasu.
Ɗan takarar gwamna na NNPP a jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da rasuwar ta cikin wata sanarwa a yau Asabar.

Cikin Sanarwar da mai magana da yawun Dan takarar gwamna kano a NNPP Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, yace Abba Gida-gida ta ce za ayi jana’izar marigayiyar a masallacin Alfurqan da ke titin Alu Avenue a cikin birnin Kano da misalin ƙarfe 4 na yamma.
Sanarwa tace Abba Gida-gida ya mika ta’aziyyar sa ga mataimakin sa a takarar gwamna bisa Wannan gagarumin rashi da yayi, Inda ya yi addu’ar Allah ya gafarta mata yasa aljanna ta zamo makomarta.