Iya Harshe: Musa Iliyasu Kwankwaso ya shiryawa yan Social media bitar sanin makamar aiki

Date:

Daga Nura Abubakar Cele

 

Dan takarar majalisar tarayya a kananan Hukumomin kura madobi da garun Mallam cikin jam’iyyar APC Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya hori duk masu tallata shi a kafafen ya sada zumunta na social media da su kaucewa cin zarafin mutane saboda banbancin jam’iyya.

 

Musa Iliyasu ya bayyana hakan ne yayin taron bita ta yini guda da ya shirya Yan social media na gidansa don koya musu dabarun yadda zasu tallata shi ba tare da cin zarafi ba.

 

Yace ya shirya musu bitar ne Saboda muhimmancin da suke da shi da Kuma koya musu dabaru na zamani na yadda ake tallan Dan takara a kafafen ba tare da sun ci zarafin wani ko wata ba, yayin da suke nasu aikin.

 

” Ina so ku Sani na dauke ku da muhimmancin gaske Kuma Ina Jin dadin yadda kuke tallata manufofin mu a wannan takara da muke yi wadda insha Allah idan muka yi nasara zamu taimakawa al’umma a kowanne bangare”. 

Talla

 

” Ina kira a gare ku da kada ku biyewa Yan hamayya wajen cin zarafin juna, ku Maida hankali wajen fadawa al’umma muhimmancin takarar mu da kuma kokarin mu na ganin mun tallafawa rayuwar al’umma ta kowacce fuska”. Inji Kwankwaso

Wani sashi na mahalarta taron bitar

 

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bukace su da su yi amfani da abubuwa da Sabbin dabarun da aka koya musu wajen cigaba da yada manufofin mu dana duk yan takarar mu na APC musamman yan takarar gwamnan jihar kano a Jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Hon Murtala Sule Garo har sukai ga gaci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Mamallakin jaridar Nigerian Tracker ya zama Ma’ajin kungiyar masu yada labarai a kafar yanar gizo ta Arewa

Kungiyar masu yada labarai a kafafen sadarwa na zamani...

Rusau: Ana zargin an harbi mutane 6 a unguwar Rimin zakara dake Kano

Daga Nazifi Dukawa   Mazauna Unguwar Rimin Zakara da ke Karamar...