Zargin dukan Malam a: Mahassada na ne suke hura wutar rikincin – Baba Ari

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Shahararren dan wasan barkwancin nan na masana’antar Kannywood Aminu Baba Ari yace mahassadansa ne suke kokarin sai sun zubar masa da kimar da yake da ita a cikin mutane, yasa suke cewa ya tattaka wata malamar Islamiyya.

 

Baba Ari ya bayyana hakan ne a wata ganawa ta musamman da yayi da Kadaura24 a Kano.

 

” Duk wanda ya zo yaga ‘yarsa a halin da na ga tawa ‘yar dole sai hankalinsa ya tashi, to Amma kuskuren da nayi shi ne nakai mata duka Kuma ban same ta ba sai na sami gefenta, Kuma na fahimci nayi kuskure na Kuma yi nadama har na baiwa malamar da iyayen ta da hukumar makarantar hakuri akan kuskuren da na yi”. Inji Baba Ari

 

Talla

Baba Ari yace bai kamata maganar ta yi nisan da ta yima Amma duk Abun da makiya suka shiga dole sai dai mutum yayi hakuri, Amma babu shakka an zalunceni da aka ce wai na yiwa malamar dukan tsiya har na tattakata Wannan magana sharrice Kuma na bar wadanda sukai min da mahaliccinmu”.

 

Yace duk wani dan unguwar Kofar Nasarawa yasan shi ba mafadaci bane Kuma baya cikin batagari a unguwar su ko masana’atar Kannywood , Amma ya fahimci akwai masu yi masa bita da kulli, Inda yace ya bar su da Allah.

 

Al’umma da dama dai sun yi mamakin yadda aka ce Aminu Baba Ari yayi wancen aikin ,Amma dai da Wannan bayani nasa watakila ya sauya yadda al’umma suka fahimci labarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...