Abubuwa 5 ne suke Kawo Rashin tsaro a Najeriya-Dr Bala Muhammad

Date:

Daga Sani Magaji Garko


 Wani malami a sashen koyar da Aikin Jarida na jami’ar Bayero ta Kano Dakta Bala Muhammad ya bayyana ginshikai guda biyar da suke Kara tabarbarewar harkokin tsaro a Najeriya.


 Dakta Bala Muhammad ya bayyana haka ne yayin taron karawa juna sani na kungiyar agaji ta Red Cross ta ICRC na kwanaki biyu kan rahoton jin kai wanda aka gudanar a Jos babban birnin jihar Filato.


 Ya ce ginshikan sune Bindigogi, Miyagun Kwayoyi, Dazuzzuka, Babur sune suke tu’azzara rashin tsaro.


 Ya ce ana yi amfani da dazuzzakan a matsayin maboyar masu aikata laifi, inda an san babu wani mutum da Zai je wajen, don Haka suke Mayar da dajin wajen fakewa idan sun aikata laifuffunsu.


 “Ka sani a musulinci muna da rukuni guda biyar wanda shahadatu Allah ilaha illallah wa’anna muhammadan rasulullah, Salloli biyar a rana, Azumi, aikin hajji da bayar da zakka. Haka kuma a binciken da na yi, rashin tsaro a Najeriya yana da ginshikai guda biyar wadanda su ne Bindigogi, Kwayoyi, daji  , Babura / ababen hawa da kariya ta tsaro “.


 Dokta Bala Muhammad wanda ke aiki aikin jarida fiye da shekaru goma ya nuna cewa in har ba’a magance tasirin waɗannan ginshiƙai ba, Nijeriya za ta ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankulan rashin tsaro.


 Ya bukaci mahalarta taron wadanda ‘yan jarida ne zalla da su nutsa wajen bincike akan matsalar kuma su yi amfani da Kafafen yada labaran da suke amfani da su don fahimtar da jama’a gaba daya.


 Gogaggen dan jaridar ya kuma ce shigo da Babur yana taimakawa Yan ta’addan wajen shiga lungu da sako wajen aiwatar da ta’addanci,ya kuma bukaci Masu Ruwa da tsaki da su Hana Shigo da Babura Cikin Kasar nan domin Magance Matsalar ta Tsaro a Kasar nan.
 Tun da farko, Kodinetan Sadarwa na kungiyar agaji ta Red Cross Society of Nigeria Mista Robin Waudo ya ce an shirya taron bitar ne domin tattaunawa da ‘yar jaridar da ke aiki a kan ayyukan ICRC da kuma kara karfin gwiwarsu kan rahoton jin kai.


 Mista Waudo ya ce a karshen bitar ana saran mahalartan su kara sani kan rahoton musabbabin rikice-rikice da hanyoyin magance kwasa-kwasan maimakon mayar da hankali kan tasirin wadannan rikice-rikicen.


 Ko’odinetan ya kuma ce za a gudanar da makamancin wannan taron bita a wannan shekarar a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya inda miliyoyin mutane  rikicin ya shafa kai tsaye ko kuma Wata fuskar.


 A wani jawabin, kakakin sadarwa na ICRC a Najeriya Aliyu Dawube ya ce taron bitar ya ta’allaka ne kan horar da dan jarida kan bayar da rahoto kan al’amuran agaji a duk lokacin da rikici ya tashi ba mai da hankali wajen yawan mutanen da aka kashe ba.


 Dawube ya ce kungiyar tasa ta bayyana dan jarida a matsayin manyan masu taka rawa wajen aiwatar da ayyukan jin kai saboda haka akwai bukatar su gano asalin musabbabin wani rikici maimakon yin rahoto kan asarar rayuka da Kai

61 COMMENTS

  1. Сериал и фильмов о Чернобыль было очень много, все они по-своему интересны. Однако именно американский канал HBO создал действительно интересный. Чернобыль сериал. Смотреть новые сериалы.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...