Buhari yace tallafin man fetur ba abu ba ne mai dorewa

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake nanata aniyarsa ta janye tallafin man fetur a 2023, yana mai cewa “ba abu ne mai ɗorewa ba idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa”.

Buhari ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da kasafin kuɗin 2023 na naira tiriliyan 20.51 ga gamayyar taron ‘yan majalisar tarayya a ranar Juma’a.

A cewarsa: “Maganar tallafin mai abu ne mai cike da cecekuce a ƙasarmu tun daga shekaraun 1980.

“Sai dai, halin da ake ciki a yanzu ya nuna cewa ba abu ne mai ɗorewa ba. A matsayinmu na ƙasa, dole ne mu tunkari batun nan da tunanin cewa akwai buƙatar mu samar da tsarin kula da sauran ɓangarori na al’umma.”

BBC Hausa sun rawaito cewa Buhari ya ce dakatar da biyan tallafin ya zama wajibi don samun kuɗin gudanar da sauran ayyuka sakamakon ƙarancin kuɗin shiga.

“Yayin da muke neman faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shigarmu, dole ne mu mayar da hankali kan yadda za mu alkinta arzikinmu.”

 Kadaura24 ta rawaito Wannan ne kasafi na ƙarshe da gwamnatin Buhari ta gabatar yayin da yake shirin sauka daga mulki a watan Mayun 2023, wanda a lokacin ne gwamnatin ke son daina biyan tallafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...