Zamu Horas da Matasa sama da 1000 gyaran waya a kano – Shugaba masu wayoyi

Date:

Daga Shehu Sulaiman Sharfadi

 

Kungiyar masu hada hadar wayoyin hannu ta jihar Kano ta sha alwashin horas da matasa dubu daya gyaran wayoyin hannu a kananan hukumomin jiharnan 44 don dogaro da kawunansu kyauta.

 

Shugaban kungiyar masu hada-hadar wayoyin hannu ta jihar kano Alhaji Ahmad Tijjani Ismail ne ya bayyana hakan a zantawarta da wakilin Kadaura24 a ofishinsa dake nan kano.

Tijjani ya bayyana cewar wannan ba shi ne karo na farko ba, a bayan kungiyar tayi nasarar horas da matasa dubu hudu a fadin jihar nan domin su samu su dogara da kansu.

 

Ya kuma bayyana cewar wannan Karon Zasu rarraba slot ga kowacce karamar hukumar jihar ta hanyar baiwa duk mai shaawar koyon gyaran wayoyin hannu zai samu dama a horas dashi.

Talla

Shugaban ya kuma bayyana cewar makasudin yin wannan horon shine don su Samar wa da dandazon matasan jiharnan aikin yi, ta yadda mutumin dake kauye yake son a gyara masa wayarsa ba sai ta kashe kudin motarsa Ya shigo cikin birni ba.

 

Kazalika Ya bayyana cewar wannan bayar da horon kungiyarsu ce ta dauki nauyi gudanar da shi a kokarinta na nuna kishin jihar da kuma matasan jiharnan dake koina afadin jihar.

 

Alhaji Ahmad ya kuma yi Kira ga gwamnatin jihar Kano kan ta mara kokarin da kungiyar baya wajen shigowa cikin wannan shiru don ceto rayuwar matasan jiharnan daga fadawa munanan dabi’u.

 

Daga karshe yayi kira ga masu cin gajiyar shirin kan su tabbata sun yi amfani da damar da suka samu ta hanyar data dace domin tsayawa da kafafunsu ta hanyar da suma nan gaba zasu iya horas da wadanda ke karkashin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...