Gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kalubalanci al’ummar Nigeria da su zauna lafiya da juna domin cigaban kasar baki daya.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummar jihar nan a yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 62 da samun ‘yancin kai wanda ya gudana a filin wasa na Sani Abacha Kano.
Yace akwai bukatar ‘yan Nigeriya su zauna da juna lafiya a matsayin ‘yan’uwa ba tare da la’akari da addini ko bambancin kabila ba.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarori da dama ta fuskar samar da ababen more rayuwa da samarwa matasa aiyukan yi da inganta fannin kiwon lafiya, ilimi da noma.
Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za a kammala ginin cibiyar cutar masu ciwon daji ta zamani yana mai ba da tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabon Asibitin .
Gwamnan ya shawarci al’ummar jihar da su guji siyasar ‘yan daba da tashe-tashen hankula, Ya roke su da su rungumi tsarin dimokuradiyya na juriya da zaman lafiya don cigaban kasar nan.
” Da yake wannan shi ne jawabina na karshe gareku a matsayi na na Gwamnan kano, ina kira ga al’ummar jihar kano da su zabi shugabannin na gari irinsu Dr. Nasiru Yusuf Gawuna Wanda nayi imani idan kuka zabe shi zai kara ciyar da Kano gaba tunda duk abun da makai da shi muka yi”.
Ganduje ya kuma yabawa dukkanin wadand sukai yi gwamna a Kano saboda irin gudunmawar da dukkaninsu suka bayar wajen cigaban jihar kano.