Daga Khadija Abdullahi
Gwamnatin China ta kaddamar da wani gangami na rage yawan kudin da ake kashewa a yayin biki da kuma rage sadaki.
Gwamnatin ta yi hakan ne a wani bangare na yunkurin dakatar da raguwar da ake samu a yawan masu aure abin da kuma ya janyo raguwar haihuwa.
Kungiyoyi da dama ne suka shiga gangamin, da nufin janyo hankalin mutane a kan rage almubazzaranci yayin biki.
Gwamnatin ta ce idan an rage yawan kudin da ake kashewa a lokacin biki za a samu karuwar masu yin aure a kasar.
To sai dai kuma masu sharhi sun ce da wuya wannan yunkuri ya yi tasiri, saboda raguwar da al’ummar kasar ke yi ya sa mutane kalilan ne zasu kai shekarun aure.