An kama wata farfesa a Abuja da laifin cin zarafin ‘yar sanda

Date:

Daga Auwal alhasan kademi

Sifeta Janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya yi tir da cin zarafin wata ‘yar sanda da uwargidanta ta yi.

An zargi Farfesa Zainab Duke Abiola da cin zarafin sifeta Teju Moses, saboda ta ki amincewa ta yi mata ayyukan da ba su shafi wadanda aka dauke ta aiki ta yi ba daga hukumar ‘yan sanda.

Kisan Ummita: Quanrong zai riƙa cin abincin ƙasarsu ne ba gabza ba — Gidan yari

Teju na aiki ne da Farfesa Zainab, wadda ma’aikaciyar shari’a ce kuma mai rajin kare hakkin dan adam a Najeriya, a matsayin odali.

Talla

Kuma lamarin ya faru ne a gidan Farfesar da ke anguwar Garki da ke Abuja ranar 20 ga watan Satumba.

Yanzu haka Farfesa Zainab da wasu yaran gidanta da ake zargi da hannu a cin zarafin na hannun rundunar ‘yan sanda inda ake ci gaba da bincike.

Nasir Ali Ahmad ya kaddamar da ginin ajujuwa 40 a karamar hukumar Nasarawa

Kazalika IGP Usman Alkali ya umurci a janye duka yan sandan da ke aiki da Farfesar.

Talla

Ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda matar da ke ikirarin kare hakkin bil adama za ta ci zarafin wani mutum, musamman wadda aka nada don ta ba ta kariya.

Kwanan nan ne rundunar yan sandan Najeriyar ta ba da sanarwar daukar matakin doka, ga duk wanda ya ci zarafin dan sanda ta ko wace siga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...