Wasu mata guda 4 sun rasu bayan kwale-kwale ya kife dasu a Jigawa

Date:

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wata yarinya ‘yar wata bakwai da wasu mata hudu bayan da kwale-kwalen su ta kife a karamar hukumar Guri.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, shi ya tabbatar da afkuwar lamarin a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin jiya Talata, inda yarinyar da kuma matan suka shiga kwale-kwale daga Nguru a jihar Yobe zuwa kauyen Adiyani na karamar hukumar Guri na jihar ta Jigawa.

“Abin takaici, kwale-kwalen ya kife suna daf da isa inda za su je. Amma matukin kwale-kwalen ya samu damar fita da ransa, yayin da su kuma fasinjojin suka nutse,” a cewar Shiisu.

Ya ce lokacin da lamarin ya faru, direbobi da ke yankin sun yi kokarin ceto fasinjojin abin bai yu ba, sai dai gano gawarwakinsu da aka yi.

BBC Hausa ta rawaito DSP Lawan ya kara da cewa an kai gawarwakin zuwa cibiyar lafiya ta Adiyani kafin babban likitan asibitin ya tabbatar da mutuwarsu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce dukkan matan da lamarin ya rutsa da su ‘yan kauyen ne na Adiyani, inda ya kuma ce an fara bincike domin gano abin da ya janyo kifewar kwale-kwalen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu Yanzu: Hukumar KNUPDA ta rushe gaban shagon jarumar Tiktok Rahama

Daga Rahama Umar Kwaru   Hukumar KNUPDA ta kaddamar da rushe...

Wata kungiya ta bukaci Gwamnan Kano ya dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Wata kungiya mai zaman kanta mai...

Kwankwaso ba zai koma APC ba – Buba Galadima

Kusa a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya karyata jita-jitar...

Yadda gwamnan Kano ya ke rabon kujerun aikin hajjin bana kamar gyada

Daga Rahama Umar Kwaru Al'ummar jihar Kano na cigaba da...