Daga Rahama Umar Kwaru
Al’ummar jihar Kano na cigaba da yabawa gwamnan jihar saboda yadda yake rabon kujerar aikin Hajjin ga rukunonin al’umma.
Kadaura24 ta rawaito tun lokacin Azumin watan Ramadana gwamnan ya rika rabon kujerun ga rukunonin al’ummar da ya rika yin bude baki da su.

Daga cikin rukunonin al’ummar da gwamnan ya rabawa kujerun makkan akwai Kungiyar shugaban ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar da yan Kannywood da marayu da dai sauransu.
Wannan lamari ya sa wasu daga cikin al’ummar jihar Kano suke yabawa gwamnan bisa wannan aiki da ke yi.
An sulhunta tsakanin Nigeria da Nijar
Wani cikin wadanda aka baiwa kungiyarsu kujerun wanda ya nemi Kadaura24 ta sakaye sunanshi, ya ce ba su taba ganin gwamnan da yake rabon kujerun aikin Hajji kamar gyada ba , tamkar gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
A Wannan ranar talata wasu daga cikin Jaruman masana’antar Kannywood suna fitowa a shafikansu na kafafen sada zumunta suna godewa gwamnan bisa yadda ya ba su kujerun aikin hajjin.
Daga cikin wadanda aka baiwa kujerun a Kannywood akwai Marubuciya a masana’antar Fauziyya D Sulaiman da Jarumai irin su Gharzali Miko da TY Shaban da KB International ( Dan gwamna).
Babu shakka daga yadda ake yi musu fatan alkhairi, Kadaura24 ta fahimci mutane da yawa sun yaba da kokarin gwamnan na ganin ya tallafawa al’ummar jihar don su sauke farali a bana.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf shi ne zai jagoranci tawagar Maniyatan bana da suka fito daga jihar.