Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnatin jihar Kano ta rusa wani katafaren gini a dake gaban gidan Sheikh Nasiru Kabara wanda ke cikin birnin Kano daura da Gidan sarki.
Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya bayar da umarnin rushe ginin bayan da bincike ya nuna cewa ana yin sa ne ba tare da izini ba a hukumar da ke da hurumin bada izinin Gina ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar a ranar Talata.
Wakiliyar kadaura24 wacce aka fara rushe ginin a kan idon ce ta rawaito cewa, an rushe ginin ne tun a daren ranar Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa akwai wata babbar kotun Kano da ta hana rushe ginin karkashin hukuncin da mai shari’a Rabi’u Sadiq ya yi.
A baya dai an sanya ranar 1 ga watan Agustan Shekarar nan da muke ciki ta 2022, matsayin ranar sauraron shari’ar, amma saboda hutun da gwamnatin jihar ta bayar a ranar Talata ne kotun ta dage zaman har zuwa ranar 4 ga watan Oktoba.
A cewar mamallakin gidan, masarautar Kano ce ta ba shi hayar filin.
“Baffa Babba Dan’agundi, wanda shi ne Manajan Darakta na Hukumar Kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano wato Karota shi ne kuma shugaban kwamitin kawar da haramtattun gine-gine ya sanar da jama’a cewa bisa rade-radin da aka yi tun da farko gwamnatin jihar Kano ko Masarauta ba ta ba da izini Gini a wurin ba.
Sanarwar ta ce yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, Gwamna Ganduje ya bada umarnin kewaye wani bangare na filin da katanga tare da fitar da wuraren shakatawa na yara a filin, yayin da sauran wuraren Kuma yace a bar shi a matsayin Filin da Yan Kadariyya za su yi amfani da shi wajen yin zikiri.
A cewar sanarwar, kwamitin ya kuma yi gargadin cewa wadanda ke gudanar da ayyuka ba bisa ka’ida ba a jihar dole ne su daina daga yanzu kamar yadda gwamnati ta kuduri aniyar gurfanar da duk wanda aka kama da laifin karya dokokin jihar game da mallakar filaye da gine-gine.
A ziyarar da kadaura24 ta kai wurin da abun ya faru da yammacin ranar talata, mun ga yadda matasa sama da 50 suna rushe ginin tare da dauke rodikan dake jikin ginin a matsayin ganima.