Jirgin kayan abinci na farko ya bar Ukraine zuwa kasuwar Duniya- MDD

Date:

Daga Halima Musa Sabaru 

 

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sanar da fara jigilar kayan abinci daga tashoshin jiragen ruwan Ukraine zuwa sauran sassan duniya, a matsayin wani gagarumin ci gaba a kokarin da ake yi wajen shawo kan hauhawar farashin kayan abinci da takin zamani a duniya.

Guterres dai na gabatar da jawabi ne jim kadan bayan da jirgin farko dauke da abinci ya tashi daga tashar ruwan Odessa da ke Ukraine bayan share tsawon watanni da dama karkashin mamayar kasar Rasha.

 

A cewar Guteress matakin da aka cimma wani muhimmin ci gaba la’akari da yadda hakan zai bai wa tarin jiragen ruwan kasuwanci damar isar da kayayyakin abinci da kuma samar da daidaito a kasuwannin abinci na duniya.

 

Talla
Talla

Yarjeneniyar jigilar abinci daga tekun Bahar Assawad dai wata dama ce ta jigilar abinci daga tashoshin ruwa uku na Ukraine wato Odessa da Chorhomask da kuma Uzny.

 

Babban magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress ya ce dukkaninmu bangarorin sun amince da fitar da kayayyakin abinci da kuma takin zamanin da Rasha ke samarwa zuwa kasuwar duniya, matakin da zai kawo sauki a game da tsada da kuma hauhawar farashin da ake fama da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...