Yanzu-Yanzu: CBN ya Karya Darajar Naira a Hukumance

Date:

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karya darajar naira a hukumance sakamakon fara aiki da ya yi da sabon tsarin canji na Nigerian Autonomous Foreign Exchange (NAFEX).

CBN ya rage darajar kuɗin da kashi 8 cikin 100, inda yanzu take N410.25 kan kowace dala ɗaya.

Kazalika bankin ya bayyana sauyin ƙarara a shafinsa.

Mako biyu da suka wuce kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa bankin zai karya darajar naira ta hanyar sauka daga kan N379 kan kowace dala ɗaya domin tsayar da farashin nairar guda ɗaya a kasuwa.

Wannan sauyin na nufin daga yanzu kasuwa ce za ta dinga fayyace darajar naira ko kuma farashinta yayin canji.

Najeriya ta daɗe tana amfani da tsaruka mabambanta wajen canjin kuɗaɗen ƙasar waje, abin da ya sa CBN ya mayar da hankali kan tsari guda ɗaya kenan a yanzu.

Babu tabbas game da yadda darajarta za ta kasance a kasuwar bayan fage, yayin da a ‘yan kwanakin nan nairar ke kaiwa har kusan N490 kan dala ɗaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...