Bikin Sallah: Ganduje ya bukaci ayi hattara, a kiyaye yayin bukukuwan Sallah

Date:

Daga Ibrahim Hussaini Dorayi


 Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bukaci jama’ar jihar, musamman musulmai da su kasance masu lura da taka-tsantsan a yayin bikin Sallah Karama.


 A cikin sakonsa na fatan alheri da Barka Sallahr bana wanda hakan ke nuna kammala azumin Ramadana, gwamnan, ta bakin kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, ya yi gargadin cewa jihar ba za ta zama mafakar samu son tada zaune tsaye ba.


 Yayinda yake bayyana tsaro a matsayin Aiki ga kowa, Ganduje ya bada tabbacin wadatarjami’an tsaro a yayin bukukuwan.


 Gwamnan ya ce, gwamnati za ta Sanya kafar wando daya ga duk wanda ke da niyyar rusa tada hankulan jama’a, sannan ya bukaci al’ummar jihar da su bai wa hukumomin tsaro muhimman bayanan da za su taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro.

 Ya yaba wa Musulmai da daukacin jama’ar jihar Kano kan yadda suka jajirce Duk da matsalolin da kasar nan ke fuskanta, inda ya bukace su da su ci gaba da addu’a kuma su ci gaba da ba gwamnati goyon baya a kokarinta na magance matsalar.


 Har ila yau, Ganduje ya umarci Musulmai da su ci gaba da kasancewa cikin farin ciki duk da Annubar  COVID-19 dake addabar kasar Inda yace ta hanyar hadin kai da gwamnati da kuma bin ka’idojin Kare Kai Daga COVID-19 wanda ya hada da wanke hannu, amfani da abin rufe fuska da kuma nisantar juna a lokacin bukukuwan Sallahr.


 Gwamnan, wanda ya yaba wa mutanen jihar Kano Dangane da irin goyon-baya da suke nuna wa gwamnatinsa ta hanyar addu’o’i, shawarwari da kuma shiga a dama da su a harkokin mulki, ya yi kira gare su da kada su gajiya wajen bayar da tasu gudummawar don wanzar da zaman lafiya da lumana a jihar.


 Sanarwar ta kuma bukaci musulman Kasar nan da su yi amfani da fa’idodin da Suka koya a watan Ramadan, wadanda suka hada da soyayya, zaman lafiya, da adalci ga rayuwar su ta yau da kullun kuma ta hakan ne suke taimakawa ci gaban kasa

164 COMMENTS

  1. Абсолютний чемпіон світу не вірить в перемогу Усика над Джошуа Усик Джошуа дивитися онлайн Антъни Джошуа и Олександър Усик минаха през официалния кантар преди очаквания с огромен интерес сблъсък помежду им. Както е известно, светът на бокса е притаил дъх в очакване на големия мач, в който на карта са

  2. Александр Усик. Подготовка к бою с Энтони Джошуа ( Subt. ) September 20, 2021 l Leave a comment l by Boxing Videos. ** FOLLOW US ON TWITTER **. Post navigation. Anthony Joshua vs. Oleksandr Usyk [ LIVE WATCHALONG – w/ Ali Drew, Barry Jones & Don Charles. Джошуа Усик смотреть онлайн Бій Усик – Джошуа за звання чемпіона світу за версією WBA, WBO та IBF відбудеться в Лондоні. Місцем його проведення стане стадіон футбольного клубу “Тоттенгем”. Щодо дати проведення бою, то

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...