Sallah: Mataimakin Gwamnan Kano ya taya al’ummar musulmi murna Sallah Karama

Date:

Daga Abubakar Sa’eed


 Mataimakin gwamnan jihar Kano Dr.Nasiru Yusuf Gawuna ya bukaci al’ummar jihar nan da su kasance masu tausayawa a duk harkokin su na mu’amala da juna yayin da suke bukukuwan karamar Sallah.

 A cewarsa … “Ina taya murna ga mai girma gwamnanmu Dr.Abdullahi Umar Ganduje da duk al’ummar musulmin jihar nan bisa kammala azumin Ramadana, daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar”.


 “Ina rokon dukkan musulmai da su ci gaba da dagewa wajen amfani da kyawawan halayen da suka koya a watan Ramadana saboda haka ina fatan al’umma zasu cigaba da addu’oin samun Zaman lafiya ga jihar Kano da Kasa baki daya.” Inji Gawuna


Cikin Wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin Gwamna Hassan Musa fagge ya aikowa Kadaura24 yace Mataimakin Gwamnan ya kuma bukace su da su ci gaba da gabatar da addu’o’in neman dawwamammen zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya tare da bin matakan kariya wadanda za su taimaka wajen dakile cutar nan ta Corona Virus.


 Yayin da yake taya daukacin musulmin jihar Kano murnar bikin karamar Sallah, mataimakin gwamnan ya kuma yabawa daukacin al’ummar jihar kan irin goyon baya da hadin kai da suke baiwa gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje yayin da take ci gaba da gudanar da shugabanci ba tare da son kai ba ta hanyar yabo. Wanda ya fito da Manufofi da shirye-shirye da nufin gina jihar Kano mai ci gaba da zaman lafiya.

72 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta sake gina Masallacin da aka kona a Gezawa

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna...

Hukumar shari’a ta Kano ta ladaftar da wasu ma’aikatan kotu

Daga Usman Hamza   Hukumar Kula da Harkokin shari'a ta Jihar...

2027: Malam Shekarau ya bayyana matsayar kungiyarsu kan hadakar yan hamayya a Nigeria

Ƙungiyar siyasa ta Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim...

Da Ɗumi-Ɗumi: Dangote ya sake rage farashin man fetur

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da ƙarin...