Mata a masana’antar kannywood dai sun maida hankali wajan yin aure a wannan lokacin inda a yanzu muka sake samin labarin cewa, jarumar masana’antar kannywood Saima Muhammad tayi aure.
Kamar yadda abokiyar sana’ar ta jaruma Rashida mai Sa’a ta wallafa sanarwar aure a shafin ta na sada zumunta instagram kamar haka.
“Alhamdulillah allah ya sanya alkairi anty saima ta amarce shekaran jiya da angonta allah ya bada zaman lafiya uwata allah yakawo yan biyu allah ya nuna mana da yan baya”.
Bayan jaruma Rashida mai Sa’a ta wallafa sanarwar a shafin nata na instagram, sai muka sami samin wata wallafar bidiyon Amarya Saima Muhammad daga shafin officialkannywood, inda suka wallafa bidiyon tare da cewa.
Amaryar jaruma Saima Muhammad Allah ya baku zaman lafiya.