Shugaban NNPP na Kano ya yi barazanar tafiya kotu bayan da uwar jam’iya ta naɗa Doguwa a matsayin shugaban riƙo

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

Shugaban Jam’iyar NNPP a Jihar Kano, Hisham Habib, ya yi barazanar ɗaukar matakin Shari’a bayan da uwar jam’iyar ta ƙasa ta ta sauke shugabannin jam’iyar na jiha.

Daily Nigerian Hausa ta fahimci cewa NNPP ta samu haɓɓaka a arewa kwanaki kaɗan bayan da sanarwar ta fita cewa tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin barin PDP zuwa jam’iyar ta NNPP.

A jiya Laraba ne Habib ya yi maraba da zuwan Kwankwaso, sai dai ya ce babu tabbacin samun takara ga sababbin shigowa jam’iyar.

A wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, Habib ya ce matakin na rushe shugabannin da uwar jam’iyar ta yi wani ƙarfa-ƙarfa ne ga dimokuraɗiyya.

Ya ce wannan matakin bai dace ba kuma ba a bi hanyar nuna domokraɗiyya na haƙiƙa ba.

Habib ya koka da cewa idan har ƴan siyasa za su riƙa shigo wa jam’iya su ture waɗanda su ke ciki, to lallai siyasa ta shiga halin tsaka mai wuya.

Sabo da haka, Habib ya ce ya fara tuntuɓa domin ɗaukar matakin Shari’a ko kuma ya fice ma da ga jami’yar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...