Karancin mai: Kamfanin NNPC ya fara lodin man fetur ga gidajen mai don magance matsalar

Date:

Daga Maryam adamu baba
 Kamfanin kula da albarkatun man fetur na kasa NNPC, ya fara lodawa manyan motoci man don rabawa ga kowanne gidajen mai domin magance karancin man da ake fama da shi a fadin kasar nan.
 Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin na NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja ranar Laraba jim kadan bayan kammala wani taro da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Kasa, NUPENG, da Kungiyar Direbobin Tankar Man Fetur ta kasa, PTD.
 Mele Kyari ya ce raba man fetur din zai kawo saukin matsanancin halin da al’umma suke ciki Saboda dogayen layukan da ake ci gaba da samu a manyan buranan kasar nan.
 “A halin yanzu, muna da sama da lita biliyan 1.7 na man fetur a hannunmu”. Inji Kyari
 “Wannan yana nufin cewa a yanzu muna da ikon yin lodi fiye da kima daga dukkan wuraren ajiyarmu.  Mun dauki gabarar tabbatar da yin lodin man sa’o’i 24 a duk wuraren ajiyar da muke dasu”.
 “Wannan zai tabbatar da magance  karancin man da Kuma wahalhalun da Yan Ƙasar nan suka fuskanta.
Shugaban Kamfanin na NNPC ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan radadin da suka fuskanta a gidajen mai, ya kuma yi kira ga masu amfani da su da su guji sayar da man fiye da Farashin da gwamnati ta kaiyade.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...