Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya kuma jigo a jam’iyyar PDP mai hamayya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce zai fice daga jam’iyyar kafin karshen wannan watan na Maris.
Tsohon gwamnan ne ya tabbatar wa BBC Hausa wannan labari, inda ya ce ya yi nisa a shirinsa na komawa jam’iyyar NNPP watau New Nigeria Peoples Party.
Wani makusancin tsohon gwamnan ya ce babu tsari a game da yadda ake tafiyar da sha’anin jam’iyyar ta PDP, lamarin da ya tilasta wa Sanata Kwankwaso tattara kayansa domin ya fice daga cikinta.
A watan jiya ne Kwankwaso ya jagoranci wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM.
Fitattun mutane da ƴan siyasa da suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wada, tsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim, tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.
A baya dai, Sanata Kwankwaso ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda jam’iyyar PDP take kokarin mayar da shi dan bora duk da gudunmawar da yake bayarwa a cikin jam’iyyar.
An dade ana kai ruwa rana tsakani tsohon gwamnan na Kano da bangaren tsohon ministan harkokin waje, Aminu Wali.
Kwankwaso ya koma jam’iyyar PDP ne daga jam’iyyar APC bayan zaben 2015, sakamakon takun-sakar da aka rika yi tsakaninsa da wanda ya gaje shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A shekarar 2019, ya tsayar da tsohon Kwamishina a gwamnatinsa, Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan jihar ta Kano, ko da yake ya sha kaye a hannun Gwamna Ganduje.