Daga Walida Nuhu Bichi
Zamu hadu da Mai Martaba Sarkin Kano, Mai Kamfanin Air Peace, Allen Onyeama
Shugaban kamfanin jirgin Air peace Mr Allen Onyema ya bayyana cewa hukumomin kamfanin zasu ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, nan ba da dadewa ba don tattaunawa kan abinda ya faru.
Kadaura24 ta rawaito idan zaku iya tunawa karshen makon da ya gabata ake musayar kalamai tsakanin fadar Sarkin Kano da Kamfanin na Air Peace.
Onyeama ya bayyana cewa ba zai bari wannan rashin fahimta ya tada kura ba saboda ya san Sarkin Kano mutum ne mai son zaman lafiya.
Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugabannin kamfanin jaridar Daily Independent.
“Ban san wannan abun ya tada hazo haka Kuma bana so Kamfanin Air Peace ya zama musababbin tada hatsaniya a kasai nan.”inji Onyeama
“Na kasance mutum mai son zaman lafiya…tun lokacin da nike da kananan shekaru don haka Zan yi abun da ya dace domin kashe Wannan fitinar.”
“Saboda haka ba zan bari ayi amfani da ni wajen raba kasar nan ba. Na dade da sanin Sarkin Kano tun yana Ciroma, lokacin da mahaifinsa ke da rai.”
“Zamu hadu wata rana, san Ba mutum ne mai son rigima ba kuma ina da tabbacin zai so ya hadu da ni kuma nima ina son haduwa da shi.”
A cewar Onyema, babu wata matsalar da wannan sabanin zai haifar.
Idan ba a mantaba Kadaura24 ta rawaito fadar Sarki Kano ta baiwa Kamfanin wa’adi kwanaki uku ko su nemi afuwar sarkin ko kuma ta dauki Matakin da ya dace akan Kamfanin.