Sarkin Kano Mutum ne mai son zaman Lafiya, zamu hadu da shi mu tattauna – Shugaban Air peace

Date:

Daga Walida Nuhu Bichi

 

Zamu hadu da Mai Martaba Sarkin Kano, Mai Kamfanin Air Peace, Allen Onyeama

Shugaban kamfanin jirgin Air peace  Mr Allen Onyema ya bayyana cewa hukumomin kamfanin zasu ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, nan ba da dadewa ba don tattaunawa kan abinda ya faru.

Kadaura24 ta rawaito idan zaku iya  tunawa  karshen makon da ya gabata ake musayar kalamai tsakanin fadar Sarkin Kano da Kamfanin na Air Peace.

Onyeama ya bayyana cewa ba zai bari wannan rashin fahimta ya tada kura ba saboda ya san Sarkin Kano mutum ne mai son zaman lafiya.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugabannin kamfanin jaridar Daily Independent.

“Ban san wannan abun ya tada hazo haka Kuma bana so Kamfanin Air Peace ya zama musababbin tada hatsaniya a kasai nan.”inji Onyeama

Na kasance mutum mai son zaman lafiya…tun lokacin da nike da kananan shekaru don haka Zan yi abun da ya dace domin kashe Wannan fitinar.”

“Saboda haka ba zan bari ayi amfani da ni wajen raba kasar nan ba. Na dade da sanin Sarkin Kano tun yana Ciroma, lokacin da mahaifinsa ke da rai.”

“Zamu hadu wata rana, san Ba mutum ne mai son rigima ba kuma ina da tabbacin zai so ya hadu da ni kuma nima ina son haduwa da shi.”

A cewar Onyema, babu wata matsalar da wannan sabanin zai haifar.

Idan ba a mantaba Kadaura24 ta rawaito fadar Sarki Kano ta baiwa Kamfanin wa’adi kwanaki uku ko su nemi afuwar sarkin ko kuma ta dauki Matakin da ya dace akan Kamfanin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...