Daga Sayyadi Abubakar
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, na shirin sake ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP.
Tuni dai Sanata Kwankwaso a ranar Talata ya gana da shugabannin jam’iyyar NNPP a wani yunkuri na kammala zuwansa jam’iyyar da ake sa ran zai yi amfani da shi wajen neman takarar shugaban kasa.
Sakataren jam’iyyar na kasa mai barin gado, Ambasada Agbo Gilbert Major ne ya bayyana hakan a Abuja, a wajen taron kwamitin zartarwar ta na kasa (NEC).
Ya ce taron na da nufin daukar muhimman shawarwari da za su mayar da jam’iyyar gabanin babban zaben 2023.
A cewarsa, nan da ‘yan kwanaki gwamnan jihar Kano da ya yi sau biyu zai koma jam’iyyar tare da abokansa.
Ya kuma yi watsi da ba Kwankwaso tikitin takarar shugaban kasa kai tsaye, inda ya ce za a bai wa sauran masu son tsayawa takara.