Ganduje ya kori wasu Ma’aikata hudu bisa laifin sayar da filaye ba bisa ka’ida ba

Date:

Daga Muhd Tasi’u
 Gwamnatin jihar Kano ta kori wasu ma’aikatan ofishin kula da filaye guda hudu da laifin sayar da kadarorin gwamnati da jabun takardu, bayar da bayanan karya da kuma gurbata bayanan Hukumar.
 Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya sanyawa hannu a ranar Talata ta nuna cewa jami’an da aka kora sun hada da Abdulmuminu Usman Magami, babban mai taimakawa safiyo dake da matakin albashi na 06 da Abdullahi Nuhu Idris, babban jami’in filaye mai matakin albashi na 10.
 Sauran sun hada da: Audu Abba Aliyu, jami’in yada labarai mai matakin albashi na 05 da kuma Baba Audu mataimakin babban jami’in filaye dake da matakin albashi na 13.
 Garba ya ce an kori jami’an ne bisa shawarar kwamitin bincike da gwamnati ta kafa, biyo bayan korafe-korafe da aka yi akansu, wanda kuma aka same su da aikata laifukan.
 Ya bayyana cewa korar su ta Yi dai-dai da Sashin na 04406 na dokokin aikin Gwamnati., inda ya kara da cewa sun yanke shawarar ne domin hakan ta zama izina ga Masu irin waccan dabi’a.
 Kwamishinan ya yi gargadin cewa gwamnatin jihar “ba za ta amince da duk wani rashin da’a daga wani ma’aikacin gwamnati ba.”
 “Saboda haka, ana sa ran dukkan ma’aikatan gwamnati su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, da amana, da inganci da kuma bin ka’idojin aikin gwamnati,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...