Mutane 12 sun kone kurmus a hanyar Kano zuwa Kaduna

Date:

Daga Aisha Abubakar Mai Agogo
 A jihar kano an yi wata arangama da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 a kauyen Tsamawa da ke karamar hukumar Garun Malam.
 A cewar Saminu Yusif Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, hatsarin ya janyo wata gobara da ta kone motar da mutanen da ke cikinta, wanda ba a iya gane su ba.
 A cewarsa, motocin kasuwancin ne guda biyu da lamarin ya rutsa da su, wata motar bus ce mai daukar fasinjoji 11 daga Zariya zuwa Kano da kuma J5 mai jigilar fasinjoji daga Kano zuwa Kaduna suka hadu.
 Sakamakon tu’azzarar gobarar, har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a tantance adadin motocin da abin ya shafa ba.
 Saminu Abdullahi ya bayyana cewa rashin bin ka’idojin hanya da na ababen hawa shi ake tunanin ya haddasa hatsarin.
 Ya roki ‘yan uwan ​​mutanen da suke tuka mota a wannan titin da su kira hukumar kashe gobara ta jihar domin tantance wadanda abin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...