Da dumi-dumi: Buhari zai tafi Ingila domin duba Lafiyar sa

Date:

Daga Tijjani Mu’azu Aujara
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa wanda ake sa ran zai dauki tsawon kwanaki goma sha hudu.
 Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasar, shi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da yasa Mata hannu a ranar Talata, Inda ya ce shugaban zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya a Kenya Gabanin ya wuce kasar ta burtaniya.
 Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Adesina ya bayyana cewa shugaban kasar zai bar Abuja ranar Talata 1 ga watan Maris domin halartar bikin cika shekaru 50 da kafa Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP@50), wanda aka shirya gudanarwa tsakanin 3 – 4 ga Maris, 2022 a Nairobi, Kenya, don girmama gayyatar da takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta ya yi masa.
 Adesina ya ce Shugaba Buhari zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Karamin Ministan Muhalli, Sharon Ikeazor, Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Maj.Gen Babagana Monguno (rtd), Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa  Hukumar, Amb. Ahmed Rufai Abubakar, da Shugabar Hukumar ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...