Ma’aikatar tsaro ta Ukraine ta wallafa saƙo a shafin Twitter inda take kira ga duka faren hula su shiga aikin soja inda ta ce ko da mutum ya haura shekara 60 ne.
A sanarwar da kwamandan dakarun ƙasar Yuri Galushkin ya fitar, abin da ake buƙata wajen ɗaukar sojan fasfo ne kaɗai da lambar ɗan ƙasa.
Tun da farko an samu ruɗani bayan an yi sanarwar sakamakon sojin sun ce mutum ko shekarunsa nawa zai iya shiga aikin, sai jama’a suka yi zaton ko ana nufin har da ƙananan yara, amma daga baya sun fito sun bayyana cewa suna nufin ko mutum ya haura shekara 60 ne zai iya shiga aikin.