Furodusa Abubakar mai shadda na shirin angwancewa da Jaruma Aisha Humaira

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman

Kyawawan hotunan kafin aure Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jaruma Aisha Ahmad Idris wacce aka fi sani da Aishatul Humaira sun karade shafukan Sada Zumunta na Facebook da Instagram a safiyar alhamis din nan.

Kadaura24 ta rawaito tun farko dai, an fara rade-radin cewa Furodusan zai angwance a watan Maris, sai dai kuma ba a bayyana wacece amaryar ba.
Da kanshi ya je shafinsa na Instagram inda ya sanar da cewa zai yi wuff da jakadiyar gishirin Dangote tare da saka hotunansu na kafin aure.
A safiyar Alhamis ne aka wayi gari da sabbin kyawawan hotunan kafin aure na furodusa a masana’antar Kannywood, Abba Bashir Maishadda da jaruma Aishatul Humaira.
Tun farko dai, shafin Labaran Kannywood a Twitter a kwanaki biyu da suka gabata sun bayyana cewa furodusan zai angwance a cikin watan Maris mai kamawa, sai dai ba a san wacece amaryar ba.
Kwatsam babu zato balle tsammani, sai ga furodusan da kansa ya wallafa hotunansa tare da jaruma Aishatul Humaira inda ya bayyana cewa aurenta zai yi.
Kamar yadda wallafar tace: “Zan yi wuff da gishiri ambassador.”
Bayan wallafar da yayi, jaruma Aishatul Humaira ta sake wallafa hotunan a shafinta na Instagram inda ta hada da alamar soyayya.
Sai dai ko bayan bayyanar hotunan, babu takamaiman lokacin auren da Furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya sanar ko kuma amarya Aishatul Humaira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...