Daga Ali kakaki
Shugaba kuma wanda ya assasa Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bai wa Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsinma dake jihar Katsina tallafin kyamarori guda biyu da kudinsu ya kai Naira miliyan uku.
Hakazalika, Farfesa Gwarzo ya ba jami’ar Dan Dicko Dan Koulodo dake Maradi da kuma Ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jamhuriyar Nijar gudunmawar kyamara daya ga kowannensu.
Farfesa Gwarzo ya sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da yake mika kayayyakin ga shugaban Jami’ar FUDMA, Farfesa Armaya’u Bichi a garin Maradi na jamhuriyar Nijar a ranar Laraba.
Shugaban Jami’ar MAAUN din da kuma shugaban Jami’ar FUDMA sun je Maradi ne domin halartar bikin rantsar da sabbin daliban Jami’ar Dan Dicko Dan Koulodo wanda ya gudana a ranar Talata 22 ga watan Fabrairu.
Da yake karbar kayayyakin, shugaban Jami’ar ta FUDMA, Farfesa Armaya’u Bichi ya godewa Farfesa Gwarzo bisa wannan karamcin.
Ya ce Jami’ar FUDMA ba ta da wata kalma da za ta iya amfani da ta wajen nuna jindadin ta game da wannan karamcin domin jami’ar ta amfana sosai da karamcin Farfesa Gwarzo,yace ko a kwanakin baya ya baiwa Jami’ar kyautar mota kirar bas da motar daukar marasa lafiya da kayayyaki ga Jami’ar.
A na sa jawabin, shugaban jam’iyyar UDDM, Farfesa Mamane Sani ya bayyana Farfesa Gwarzo a matsayin mutum mai jajircewa da sadaukarwa wajen bunkasa ilimi a nahiyar Afrika baki daya tare da yaba masa bisa tallafin da yake bai wa jami’ar.
Shi ma da yake nasa jawabin, Ministan Ilimi mai zurfi na Jamhuriyar Nijar, Dokta Mamoudou Djibo ya yabawa Farfesa Gwarzo bisa gudummawar kyamarar da ya bai wa sashen yada labarai na ma’aikatar.
Ministan wanda ya mika godiyarsa ga Farfesa Gwarzo bisa wannan karamcin, ya ce Jamhuriyar Nijar na alfahari da Farfesa Gwarzo bisa gagarumin tallafin da yake bai wa fannin ilimi a kasar, ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya saka masa da alheri.
Kazalika, hukumar gudanarwa ta Jami’ar Dan Dicko Dan Koulodo dake Maradi sun karrama shugaban ƙungiyar jami’o’i masu zaman kansu ta Afirka, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wanda kuma har wala yau shi ne shugaba wanda ya kafa jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer da Nijeriya.
Shugaban jami’ar UDDM, Farfesa Mamane Sani ya ce sun dauki matakin karrama Farfesa Gwarzo ne da lambar yabo ta karramawa bisa taimakon da Farfesa Gwarzo ke bai wa Jami’ar ta UDDM.