Daga Abdullahi kano
Makarantar Islammiya ta Madrasatu Zubairu Bin Awwam Litahfizil Qur’an Waddarasatil Islamiyya da ke Unguwar Tunga a karamar hukumar Gwale na neman gudun muwar Bayin Allah domin a siya mata wani kango a unguwar don yin matsuguninta na din din din.
Shugaban Makarantar Malam Abdulrazak Zubairu(Malam Baffa) ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi yayin bikin saukar Dalibai Goma, wanda makarantar islamiyyar ta gudanar a unguwar Tunga , karamar Hukumar Gwale Kano.
Yace makarantar ta sami Albarkar dalibai , inda a kullum dalibai sai karuwa suke sai dai rashin wadataccen Muhalli na kawo tarnaki a fannin cigaban da koyar da dalibai ilmin addinin musulunci.
“Muna amfani da wani gida , da kuma kofar gidajen alumma a matsayin ajujuwa to lokacin damina da sanyi muna fuskantar kalubale, wasu magada sun bamu aron kangonsu muna koyar da dalibai a ciki, amma yanzu suna bukatar za su siyar, akan kudi Naira miliyan daya da Rabi.”
” Muna rokon Bayan Allah wadanda Allah ya horewa , a taimaka a siya mana wannan kangon, domin wata kungiya tayi mana alkawarin indai mun mallaki filin, za su gina mana ajujuwa fi sabi lillah” inji malam Baffa.
Ga duk Mai bukatar taimakawa zai iya tuntubar malam baffa , Tunga a kan wadannan lambobi +234 813 660 8606
Yayin bikin saukar karatun Alqur’ani mai girma na dalibai goma, an gudanar da jawabai na Jan hankali da nasihohi don samar da alumma ta Gari.