Ra’ayi :Kafafen yada labarai na yiwa Gwamna Ganduje ado da lambar yabo – Inji Aminu Dahiru

Date:

 Daga Aminu Dahiru
 Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya koma gida da wata lambar yabo wadda Kungiyar mamallaka Kafofin yada labarai na Arewacin Najeriya suka baiwa gwamnan Saboda cancantar sa.
 A ranar Litinin din da ta gabata a taronta na shekara karo na 7 da aka gudanar Bristol Palace, da ke birnin Kano, kungiyar mamallaka kafafen yada labarai ta Arewa NBMOA ta bayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ‘Gwamnan da ya fi kowanne gwamnna yawan kafafen yada labarai a jihar da in banda Jihar Lagos.
 Da yake mika lambar yabon ga gwamnan, Shugaban kungiyar Alhaji Abdullahi Yelwa, wanda ya yaba da kyawawan halaye na gwamnan, ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya kulla kyakykyawar alaka tsakanin gwamnatinsa da kafafen yada labarai.
Tun lokacin da ya hau mulki a shekarar 2015, taken Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bada tabbacin zai samar da yanayi mai kyau da kuma tallafa muku yan Jaridu don su samun ci gaba a aikinsu.”
 Gwamnan ya yi imanin cewa “a matsayin Kafafen yada labaran durka ta hudu a mulkin demokaradiyya, yace kafofin suna taka muhimmiyar rawa a cikin dimokuradiyya da ci gaban kasa.”
 Ba wannan kadai ba, gwamnan ya kasance daya daga cikin manyan masu fafutukar kare hakkin yan Jaridu a kasar nan, daga lokaci zuwa lokaci gwamnati na horar da ‘yan jarida tare da ba su damammaki daban-daban.
 Tun hawan da gwamnati zuwa yau babu wani dan jarida da aka ci zarafinsa ko aka hana shi gudanar da aikinsa yadda ya dace, Wannan wata dama ce da a kano ne kadai ta Samu.
 Duk da haka, don nuna da yadda ya damu da kafafen yada labarai, gwamnan ya busawa Kamfanin buga Jarida na Triumph, bayan rufe ta da gwamnatin data gabata ta yi na rufe Kamfanin ba tare da wani  dalili ba.
 Bugu da kari, gidan talabijin na Abubakar Rimi da gidan rediyon jihar Kano sun shiga sahun Kafafen yada labaran da suke gogayya Saboda Kayan aiki na Zamani da Kuma hawa Sabon tsarin yada labarai da ya dorasa su a kai.
 Ya kamata sauran gwamnonin jihohin kasar nan su yi koyi da Gwamna Ganduje don amfanin al’ummar su.
 Aminu Dahiru Shi ne Babban Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Kano akan Hoto
 Fabrairu 23, 2022

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...