Daga Maryam Muhd
Da sanyin safiyar Wannan rana gobara ta tashi hedkwatar ma’aikatar kudi ta tarayya da ke Abuja.
Kadaura24 ta rawaito Ginin yana cikin Babbar Cibiyar Kasuwanci, kusa da Sakatariyar Tarayya wadda ke da sauran Ma’aikatu da Hukumomin gwamnati a babban birnin kasar.
Kakakin hukumar kashe gobara ta tarayya dake Abuja Abraham Paul a ranar Laraba ya tabbatar da faruwar lamarin.
Paul ya ce an tura jami’an hukumar kashe gobara zuwa wurin domin shawo Kan lamarin.