Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Cristiano Ronaldo ya shirya komawa Paris Saint-German a karshen kakar nan.
Ronaldo dai yana samun kira daga PSG, Saboda suna shirya tsarin sallamar mai horas da Kungiyar Pochetteno su maye gurbin sa da tsohon kociyan Real Madrid Zinidine Zidane.
A cewar gidan jaridar El Chiringuito, Zidane wanda zai iya kasancewa kociyan PSG, Yana son yayi aiki tare da Cristiano Ronaldo a kungiyar.
Bayan Zidane ya karbi tabbacin cewar Neymar Jr da Lionel Messi zasu cigaba da zama a kungiyar hakan yasa yake son hadasu da Cristiano Ronaldo suyi wasa tare.
Ronaldo dai yana fuskantar matsi a Manchester United, Inda ake ganin idan har kungiyar ta gaza samun gurbin fafatawa agasar zakarun nahiyar turai shekara mai zuwa to babu makawa zai raba gari dasu.