Daga Kamal Yahaya Zakariyya
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai tafi kasashen Gambia da Senegal domin gudanar da ziyarar aiki ta mako guda Sakamakon gayyatar da majalisar dattawan kasar Gambia ta yi masa.
Wata sanarwa da Masarautar kano ta fitar ta ce, matakin farko na ziyarar da za ta kai shi Gambiya za ta ba shi damar halartar bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kan kasar wanda za a gudanar a ranar Juma’a a matsayin babban bako na musamman. Har ila yau, Alhaji Aminu Ado Bayero zai gana da ‘yan kasuwar Gambiya.
An kuma shirya Sarkin zai halarci Sallar Juma’a tare da Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow daga bisani kuma ya kai masa ziyarar ban girma.
Ziyarar a Gambia za ta kare ne da gagarumin liyafar karrama da majalisar dattawan kasar ta Gambia za ta shiryawa Sarkin na kano.
Sarkin, Alhaji Aminu Ado Bayero, zai samu rakiyar Ambasada Ahmed Umar, Dan Malikin Kano, Isa Sanusi, shugaban cibiyar Kasuwanci ta Kano, Alhaji Dalhatu Abubakar da wasu jami’an cibiyar guda biyu, za su wuce Dakar babban birnin kasar Senegal. inda kuma ake sa ran sarkin zai kai ziyarar ban girma ga shugaban kasar Senegal Mr. Macky Sall.