Sarkin Kano Aminu Ado zai ziyarci kasashen Senegal da Gambia

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakariyya
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai tafi kasashen Gambia da Senegal domin gudanar da ziyarar aiki ta mako guda Sakamakon gayyatar da majalisar dattawan kasar Gambia ta yi masa.
 Wata sanarwa da Masarautar kano ta fitar ta ce, matakin farko na ziyarar da za ta kai shi Gambiya za ta ba shi damar halartar bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kan kasar wanda za a gudanar a ranar Juma’a a matsayin babban bako na musamman. Har ila yau, Alhaji Aminu Ado Bayero zai gana da ‘yan kasuwar Gambiya.
 An kuma shirya Sarkin zai halarci Sallar Juma’a tare da Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow daga bisani kuma ya kai masa ziyarar ban girma.
 Ziyarar a Gambia za ta kare ne da gagarumin liyafar karrama da majalisar dattawan kasar ta Gambia za ta shiryawa Sarkin na kano.
 Sarkin, Alhaji Aminu Ado Bayero, zai samu rakiyar Ambasada Ahmed Umar, Dan Malikin Kano, Isa Sanusi, shugaban cibiyar Kasuwanci ta Kano, Alhaji Dalhatu Abubakar da wasu jami’an cibiyar guda biyu, za su wuce Dakar babban birnin kasar Senegal.  inda kuma ake sa ran sarkin zai kai ziyarar ban girma ga shugaban kasar Senegal Mr. Macky Sall.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da nuna tallan maganin Gargajiya a Fina-finai da yawo a tituna

A wani mataki na tabbatar da bin ka'idoji tare...

Da dumi-dumi: NNPP ta nemi afuwar Tinubu kan kalaman suka da ake zargin Kwankwaso ya yi masa

  Jam’iyyar NNPP ta nemi afuwar Shugaban kasa Bola Tinubu...

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...