Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kwamitin kula da lafiyar kwakwalwa na jihar Kano ya gudanar da taron tattaunawa na kwana daya da kungiyoyin mata, kungiyoyi masu zaman kansu, da masu hannu da shuni, domin tattauna batutuwan da suka shafi lafiyar kwakwalwa da kuma yadda za a Sami cigaba a fannin.
Kadaura24 ta rawaito Shugabar Kwamitin Dr Fauziyya Buba Idris ta bayyana haka a taron tattaunawa kan lafiyar kwakwalwa karo na uku da kungiyoyin mata wanda aka gudanar a Kano.
Dokta Fauziyya wacce kuma mai ba da shawara ta musamman ce ga gwamna kan harkokin kiwon lafiya kuma shugabar jakadun mata na yaki da shan miyagun kwayoyi ta jihar ta ce an wayar da kan jama’a ne da nufin samar da mafita mai ɗorewa a kan wannan annoba da ta addabi al’umma inda tace hakan Zai iya Zama rigakafin annobar.
Cikin Wata sanarwa da Jami’in yada labaran Ofishin S A Health Auwal Musa Yola ya aikowa Kadaura24 yace Dr. Buba ta bayyana matsalar tabin hankali a matsayin daya daga cikin batutuwan da suka shafi kiwon lafiya domin galibin mutane ba sa ba shi fifiko sosai kuma galibi suna kyamar wadanda abin ya shafa.
Dr. Fauziyya ta yi nuni da cewa kwamitocin ya sanyawa masu ruwa da tsaki Waɗanda suka hadar da iyaye masu hannu da shunk, masu rike da sarautun gargajiya, jami’an gwamnati da kungiyoyin mata da dai Sauran a Cikin lamarin don tsara hanyoyin magance matsalar tabin hankali, shaye-shayen miyagun kwayoyi da cin zarafin ‘ya’ya mata.
Dokta Fauziyya Buba ta kara da cewa gwamnatin jihar ta amince da shawarwarin daga zaman tattaunawar da akai a karon farko da na biyu, wanda ya haifar da sakamako mai kyau.
Ita ma a nata jawabin, kwararriyar mai kula da yara kanana ta Unicef hajiya Fatima Adamu wadda ta yi kira da a sanya maza a cikin tattaunawar, ta ce maza na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen dakile Matsalolin da suke addabar al’umma.
Ta kara da cewa sashin kare hakkin yara na Unicef ya samar da ayyuka da dama ga yaran dake gararanba a kan titi tare da tallafawa cibiyoyin da dama da suke tallafawa rayuwar Kananan yara.
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka yi jawabai a zaurukan taron sun hada da Haj. Nafisa Ado daga FCDO, haj. Mairo Bello daga AHIP, Barista Maimuna Sharif daga WOLBI, Hussaina Ahmad daga KACCIMA, da dai sauransu.
Sun alakanta matsalolin lafiyar kwakwalwa da shaye-shaye, fyade, rashin aikinyi da rashin zuwa makarantu.