MOPPAN ta Sulhunta yan wasan kannywood

Date:

Daga Aisha Aliyu Muhd

 

Rahotannin daga masana’antar shirya Fina-finan Hausa ta kannywood sun bayyana cewar an yi sulhu a tsakanin jaruman Kannywood bisa wata yar gajeriyar sa-in-sa a tsakanin su day aka samu a makon jiya.

Kadaura24 ta rawaito Rahotan yace tsofaffin Jaruman Kannywood ɗin Kabiru Mai Kaba da Ibrahim Mandawari da Shugaban MOPPON Ahmad Sarari, ne suka jagoranci kwamitin sulhun.

Kamar yadda rahotan ya riske mu, tsofaffin jaruman ne suka shiga maganar ganin cewar rigimar tana nema ta wuce gona da iri, a saboda haka ne suka yi gaggawar sulhu a tsakanin jaruman.

An ruwaito cewar an yi sulhun ne a gidan mawakin tsohon sarkin Kano Naziru Ahmad Sarkin waka, dake Jihar Kano da magaribar yau litinin, kuma a dukkan alamu an Sami dai-daito.

A lokacin zaman Sulhun akwai Naziru Sarkin waka da Abubakar Bashir Mai Shadda da Mustapha na Baraska da Musbahu Ahmad da Hadiza Mohammed da jagororin sulhu da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Naziru Sarkin waka da Abubakar Bashir Mai Shadda a Shafukan su na Facebook  sun bayyanda cewa Sulhu alkhairi ne, Kuma sun yi kalamai da suke tabbatar da cewa kowanne su ya amince da sulhun da akai yi musu.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito an Fara Samun sabani ne tsakanin Yan masana’antar ta kannywood bisa kalaman da Ladin cima tayi Kan kudin da ake biyanta idan ta yi fim.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...