Wasu Yara biyu sun Rasa Rayukansu a wani kududdufi a Mariri

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

Wasu Mutane biyu, Umar Auwalu mai shekaru 15 da Muhammed Nafis, 20, a ranar Juma’a sun Rasa Rayukansu a cikin wani kududdufi a Mariri Ramin Kalanzir da ke karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Alhaji Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Kano.

Abdullahi ya ce hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 07:57 na safe daga wani mai suna Mustapha Musa inda nan take ta aika da jami’an ta zuwa inda lamarin ya faru da misalin karfe 08:10 na safe.

“An fitar da su daga cikin kududdufin kuma daga baya an mika gawarwakinsu ga Dagacin unguwar Sheka Gabas, Alhaji Umar Yunusa,” in ji Abdullahi.

Jami’in Hulda da jama’a na hukumar kashe gobarar ya ce har yanzu ba a gano musabbabin mutuwar su ba, amma ana ci gaba da bincike.

Ya shawarci iyayen yara da kuma masu unguwanni dsu Rika kula da zirga-zirgar ya’yansu a musamman ga wadanda suke kusa da kududdufi don hana faruwar abubuwa irin wadannan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...