Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhassan ta Rasu.
Wata majiya mai tushe ta fadawa Solacebase cewa ta Rasu a ranar Juma’a a wani asibitin Alkahira, Masar bayan rashin lafiya.
Aisha Jummai Al-Hassan wacce aka fi sani da “Mama Taraba” tsohuwar Sanata ce, daga yankin Sanatan Arewacin Taraba.
Ita ce ‘Yar takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC a zaben 2015. Ta tsaya takarar Gwamna karkashin inuwar UDP a zaben 2019.
An haifi Aisha Jummai Al-Hassan a ranar 16 ga Satumba, 1959 a Jalingo, jihar Taraba
Allah ya jikanta yai mata rahama ya kyautata namu zuwan