Buhari Ya Amince Da kafa Kwamitin Bincike a Kan Hadiza Bala Usman

Date:

Daga Safiyya Abbas


 Shugaba Buhari ya amince da shawarar da Ma’aikatar Sufuri a karkashin Rotimi Amaechi ta bayar na kafa kwamitin bincike da zai binciki yadda ake gudanar da Hukumar Kula da Tashar Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA).


 Shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Garba Shehu, ya kuma amince da cewa Manajan Darakta, Hadiza Bala Usman ta koma gefe yayin da ake gudanar da bincike, sannan Mohammed Koko zai rike mukamin a Matsayin Mai rukon kwaryar .


 Daraktan, Ma’aikatar Kula da zirga-zirgar jiragen Ruwa ne zai jagoranci kwamitin yayin da Mataimakin Daraktan Harkokin Shari’a na ma’aikatar shi zai  zama Sakatare.


 Sanarwar tace Minista Rotimi Shi Zai sanar da Sauran mambobin kwamitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...

Sarkin Yaƙin Garko, ya ɗauki nauyin dubawa da raba magunguna kyauta ga marasa lafiyar 1400 a Garko

  Sarkin Yaƙin Garko, mai kishin al'umma, kuma ɗan jam'iyyar...

NAHCON ta yi jigilar Maniyatan Nigeria Sama da 24,000 zuwa Saudiyya a kwanaki 10

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar Kula da aikin hajji ta...