Gobara ta kone ofishin Rigakafi na karamar Hukumar Rogo kurmus

Date:

Rukayya Abdullahi Maida
A ranar Lahadin da ta gabata ne gobara ta kone ofishin rigakafi na kasa (NPI) dake karamar hukumar Rogo kurmos
 A jawabinsa a lokacin da yake karbar wata tawaga mai karfi daga hukumar kula da lafiya a matakin farko shugaban karamar hukumar Rogo Alh Mubarak Bashir Fulatan wanda mataimakins shugaban karamar hukumar Alhaji Sabiu Surajo Rogo ya wakilta ya bayyana cewa gobara har yanzu ba a san musabbabin tashin ta ba, ta lalata
Wuraren adana alluran rigakafi, Muhimman takardu da kuma ginin baki.
 Ya kuma bayyana cewa, karamar hukumar a nata bangaren ta ba da umarnin sashin aiyuka na karamar Hukumar domin tattara rahoton barnar da gobarar ta yi, domin baiwa karamar hukumar damar daukar matakan da suka dace.
Cikin Wata sanarwa da Jami’in hulda da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya Matakin farko ta Jihar Kano Maikudi Muhd marafa ya aikowa Kadaura24, yace Tun da farko a nasa jawabin, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko ta jiha Dr. Tijjani Hussain wanda ya samu wakilcin Manajan shirin SERICC Dr. Habib Tijjani Gwarzo ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici Matuka.
Ya kuma bayyana Cewa gobarar ta kawo koma baya ga ayyukan rigakafi na yau da kullun a yankin.
 Dr. Tijjani ba ba da tabbacin cewa, za a dauki dukkan matakan da suka dace don samar da matakan gaggawa bayan tattara rahoton da Kwamitin ya tantance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...