Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Wani matashi Mai Suna John ya shiga addinin Musulci Sakamakon Kallon Shirin nan Mai Dogon zango Mai Suna Izzar so .
Kadaura24 ta rawaito Mashiryin Kuma Jarumi a Cikin Shirin na Izzar so Lawan Ahmad ne ya bayyana hakan a sashin shafinsa na Facebook.
“Masha Allah A Yaune Mukayi Babban Kamu A Musulunci Inda Wannan Bawan Allah Ya Shiga Musulunci Saboda Kallon IZZAR SO Da Yakeyi, Tun Daga Cross river, idom Ikon Local Government Cross River Yanzu Haka Dai Ya Karbi Musulunci, Kuma Yanzu Haka Sunansa Ya koma Umar Daga John, Munayi Masa Addu a Allah Yasa Ya shigo Addinin musulunci A Sa a Allah Yasa Ya Amfane Shi, Amin” inii Ahmad Lawan
Al’umma da dama dai Suna Kallon Shirin ne na Izzar so Saboda yadda yake fadakarwa ta fuskar addinin Musulci da riko da Gaskiya da Amana.
Hahaha kaji wane wasan yara addini ma ya zama wasan kallo kenan wannan a raini hankali ma was zaku Yi wasa dashe