Daga Zaiyad Isma’il Yola
Wani mai neman zama dan takarar gwamnan jihar adamawa a tutar jam’iyyar APC mai suna Alhaji Ahmadu Hamma nasara ya yi alkawarin farfado da masana’antu jihar Adamawa idon nasamu damar kasancewa gwamnan jihar a shekara ta 2023 .
Alhaji Ahmadu Hamman Nasara Dan Maje Adamawa kana ciroman Jimeta ne ya furta hakan a zantawarsa da kafar Zij online TV a yola.
Dan maje yace idan jama’ar jihar sun bashi kuri’unsu, zai maganace musu matsalolin da jihar ke fama dasu, ta hanyar samar musu da kayiyakin more rayuwa domin suma su sharbi romon demokradiya.
Kadaura24 ta rawaito da yake bayyana gogayyarsa a fagen kasuwancin, dan maje yace ya shiga harkan kasuwancin tun yana da shekaru18, don haka zai yi amfani da kwarewarsa ta fusakar kasuwanci wujen tsamo jihar Adamawa daga matsalolin tattalin arzikin da suka addabeta .
” Nayi amanna da wannan shiri nawa na farfado da masana’antu a jiharmu, zamu samarwa matasa da mata abubuwa. dogaro da Kanwunasu domin babu wata al’umma da take samun cigaba ba tare da matasanta suna dogaro da kawunansu ba” Inji Ahmadu Hamman
A karshe dan maje yace zai samarwa mata sana’o’in yi wanda zasu rika yin kasuwancin daga gidajensu, Wanda yin hakan zai basu damar samun su dogaro da Kawunansu.