Dalar Shinkafa: Farashin shinkafa zai sauko nan ba da jimawa ba, in ji RIFAN

Date:

Daga Zara jamil Isa
 Kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya, RIFAN, ta ce an kammala shirin kaddamar da buhunan shinkafa miliyan daya da aka jibge a matsayin dalar shinkafa wanda ake sa ran shugaban kasa muhd buhari zai a Abuja ranar Talata.
 Shehu Muazu, shugaban kwamitin dalar shinkafar, RIFAN ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa dalar shinkafa ya nuna cewa akwai yuwuwar samar da abinci a kasar nan.
 A cewar Muazu, bayan kaddamar da dala, babban bankin Najeriya da RIFAN za su ware shinkafar ga masu sarrafa shinkafa yan gida domin gyarata.
 RIFAN tare da hadin gwiwar kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Najeriya za su sarrafa shinkafar tare da sayar da ita a kan farashi mai rahusa.
 “Wannan zai haifar da raguwar farashin shinkafar da zarar ta fara shiga cikin kasuwanni.
 “kungiyar da ƙungiyar masu masana’antun shinkafa sun yi yarjejeniyar cewa za mu sayar wa ‘yan Nijeriya shinkafa akan farashi mai rahusa.
 “labari mai dadi shi ne shinkafa za ta zamo mafi saukin araha cikin kayayyakin abinchi saboda nasarar da aka samu a tsarin, ”in ji shi.
 Mista Muazu ya kuma kara da cewa, shirin Anchor Borrower’s, ABP, wanda aka yi shi domin taimakawa kananan manoma, ya tabbatar da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na magance matsalar karanci da tsadar  abinci a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...