An dakatar da Hadiza Bala Usman a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA).
An fara nada ta ne a 2016 bayan korar Habib Abdullahi wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da wa’adinsa na biyu.
Babu wani dalili da aka bayar na dakatar da Hadiza Bala Usman wanda aka sake nada ta a karo na biyu a watan Janairu.
Wata majiya a Ma’aikatar Sufuri, wacce ke kula da NPA, ta yi ishara da cewa Akwai takun saka tsakanin Ministan, Chibuike Rotimi Amaechi, da Usman a ‘yan kwanakin nan.
Majiyar, wacce kuma mataimaki ce ga Ministan, ta ce Amaechi ya damu matuka da halin wuce gona da iri na Hadiza Usman.
“Ee, an dakatar da MD a safiyar ranar Alhamis amma Ministan zai bayar da cikakken bayani a ranar Juma’a.
“Ministan da wasu mambobin ma’aikatar suna Jos a halin yanzu don wani shiri kuma an shirya zai yi wa manema labarai bayani game da batun.
“Ba a ba da dalilin dakatar da ita ba amma ina iya tabbatar muku da cewa an dakatar da ita,” in ji shi