Al’ummar Unguwar Yamadawa a Kano sun kama Yan Bindiga 2

Date:

Abdulrashid B Imam

Mazauna Unguwar Yamadawa, Ɗorayi Babba da ke karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano sun kame wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne yayin da suke kokarin yi wa wani mutum fashi a yankin da misalin karfe 11.00 na daren Laraba.
 Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne a daren Laraba bayan da wadanda ake zargin su biyu suka fito da bindiga a kokarin yi wa wani mutum fashi a yayin da suka tuka mota zuwa gidansa.

 Sun ce lamarin ya ja hankalin mutanen da ke kusa kuma nan da nan suka fada kan ‘yan bindigar wadanda suka bude wuta kuma suka yi yunkurin tserewa da keken mai kafa uku.
 Sai dai kuma mutanen sun yi fito-na-fito da ‘yan bindigan, sun kame su tare da mika su ga‘ yan sanda da ke yankin.


 A cewar daya daga cikin shaidun, ‘yan sanda sun tafi da wadanda ake zargin zuwa asibiti saboda mummunar azabtar da su da mazauna yankin suka yi musu.


 Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cafke wadanda ake zargin‘ yan fashin ne a ranar Alhamis.


 Ya ce an samu bindiga da wuka daga wanda ake zargin a yayin da suke kokarin kwace wata mota kirar Toyota Corolla

351 COMMENTS

  1. 07:40. Болельщики считают, что Усик побьёт Джошуа. Комментирует Эдди Хирн. 25.08.21. 19:10. Энтони Джошуа сравнил себя с Месси и рассказал о подготовке к Усику. 24.08.21. 13:05. Энтони Джошуа назвал ключ к Джошуа Усик смотреть онлайн Усик против Джошуа – Костя Цзю

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...