Daga Aisha Mai Agogo
A ranar Litinin din nan ne tsohon kwamishinan ayyuka na Kano, Engr Muaz Magaji ya koka kan shirin gwamnatin jihar Kano na tauye masa hakkinsa ta hanyar amfani da jami’an ‘yan sanda.
Muaz Magaji wanda ya taba rike mukamin kwamishina da kuma shugaban wani kwamiti a gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa “A kwanakin baya, a hukumance an gayyace ni sashin SIB rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano bisa zargin da nake jira na ji!”.
A wani abun da ya rubuta ga mabiyan sa na Facebook, mai sukar lamarin ya ce “Gwamnatin Kano ta dauki matakin tsoratar dani ta hanyar amfani da jami’an ‘yan sandan jihar kano”.
“Bayan kasa rufe shafina na Facebook, gwamnatin jihar Kano ta dauki matakin tsoratarwa ta hanyar amfani da jami’an ‘yan sandan jihar.” Kamar yadda muaz magaji ya rubuta a shafinsa
Ya bayyana cewa “.. A kwanakin baya an gayyace ni a hukumance zuwa sashin siyasa na SIB, Kano bisa zargin da har yanzu ba fadamin ba!”
Da yake mayar da martani kan lamarin da ya kunno kai, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi ikirarin cewa ya baisan da faruwar wannan wasan kwaikwayo da ya kunno kai.
Sai dai ya roki a ba shi lokaci domin ya gudanar da bincike kan gaskiyar lamarin ko akasin haka tare da alkawarin yiwa manema labarai bayani nan ba da jimawa ba
Asl